Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti na shekarar 2026.
Jami’ar da ke kula da tattara sakamakon zaben, Farfesa Adenike Oladiji, ta sanar da sakamakon da sanyin safiyar Lahadi, inda ta ce Oyebanji ya samu kuri’u 319,224, inda ya doke abokan hamayyarsa.
Dan takarar jam’iyyar PDP, Oluwole Oluyede, ya samu kuri’u 40,543, yayin da Dare Bejide na jam’iyyar ADP ya samu kuri’u 12,872.
INEC ta bayyana cewa an tantance masu kada kuri’a 384,940, inda aka samu sahihan kuri’u 375,777.
An fara kada kuri’a da misalin karfe 8:31 na safe ranar Asabar, sannan aka kammala da misalin 2:30 na rana, inda dubban jama’a suka fito kada kuri’a a kananan hukumomin jihar guda 16.
Sakamakon ya nuna cewa jam’iyyar APC ta Oyebanji ta yi nasara a mafi yawan kananan hukumomi, ciki har da Ado, Ekiti West, Ijero, Ikole da Ekiti East.
An tattara sakamakon zaben ne a cibiyar tattara sakamako ta jihar kafin INEC ta kammala sanar da wanda ya lashe zaben.

0 $type={blogger}:
Post a Comment