Likitocin Najeriya sun yi gargadin cewa tsarin kiwon lafiyar ƙasar na fuskantar matsalar ƙarancin ma’aikata mai tsanani, inda kusan likitoci 55,000 ne kacal suka rage domin kula da al’umma fiye da miliyan 220.
Sun bayyana haka ne a taron ƙungiyar likitocin da ke aikin horo (ARD) na Asibitin Hauka na Tarayya da ke Yaba, Lagos, mai taken: “Likitoci kaɗan, marasa lafiya da yawa: Illar ƙarancin ma’aikata ga lafiyar tunanin ‘yan Najeriya.”
Likitocin sun ce matsalar ficewar ma’aikata zuwa ƙasashen waje ta ƙara ta’azzara matsalar kiwon lafiya, musamman bangaren kula da lafiyar kwakwalwa.
Sun bayyana cewa fiye da likitocin Najeriya 16,000 sun bar ƙasar a cikin shekaru biyar da suka gabata, lamarin da ya ƙara rage yawan ma’aikatan lafiya.
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Farfesa Omoti Ernest, ya ce duk da cewa akwai sama da likitoci 130,000 da aka yi rajista a Najeriya, kusan 55,000 ne kawai ke aiki a cikin ƙasar.
Ya ce hakan na nufin akwai likita kusan guda ɗaya ga mutane 3,600 zuwa 4,000, wanda ya yi ƙasa sosai da ƙa’idar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadda ta ke ba da shawarar likita ɗaya ga mutane kusan 600.
Masana sun ce ficewar likitoci zuwa ƙasashen kamar Birtaniya da Kanada da Amurka na faruwa ne saboda ƙarancin albashi da rashin kayan aiki da rashin tsaro da ƙarancin damar ci gaba a aiki.
Sun kuma yi gargadin cewa matsalar ta fi shafar bangaren lafiyar kwakwalwa, inda sama da mutane miliyan 40 ke fama da matsalolin tunani a Najeriya, amma kusan kashi 85 cikin 100 ba sa samun kulawar da ta dace.
Shugabar ƙungiyar masu kula da lafiyar kwakwalwa ta Najeriya, Dakta Veronica Nyamali, ta ce ƙasar na da ƙasa da likitocin kwakwalwa 150, abin da ke sa magani ya yi tsada kuma ya yi wahalar samu.
Ta yi kira ga gwamnati da ta ƙara albashi da jin daɗin ma’aikatan lafiya da inganta asibitoci da samar da kayan aiki da ƙirƙirar hanyoyin da za su sa likitoci su ci gaba da aiki a Najeriya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment