Kotun Koriya ta Kudu Ta Yanke Wa Uwargidan Tsohon Shugaban Ƙasar Hukuncin Shekaru Bakwai a Gidan Yari Saboda Da Hanci.

Kotun Koriya ta Kudu Ta Yanke Wa  Uwargidan Tsohon Shugaban Ƙasar Hukuncin Shekaru Bakwai a Gidan Yari Saboda Da Hanci.

Kotun Koriya ta Kudu ta yanke wa  uwargidan tsohon shugaban ƙasar, Kim Keon Hee, hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bayan samunta da laifin karɓar cin hanci da kyaututtuka masu tsada domin taimaka wa wasu ta fuskar siyasa.

Kotun Babban Gundumar Seoul ta ce Kim ta karɓi kayan ado masu tsada da jaka ta alfarma da sauran kyaututtuka daga wasu mutane da ke neman samun gata da taimako a lokacin da mijinta, Yoon Suk Yeol, yake kan mulki.

Alƙalin kotun ya bayyana cewa Kim ta yi amfani da matsayinta na uwargidan shugaban ƙasa wajen bayar da damar samun ayyuka da wasu al’amuran kasuwanci.

An kuma ci ta tarar won miliyan 64.8 (kimanin dala dubu 42), sannan kotun ta bayar da umarnin ƙwace abubuwan da aka karɓa.

Kim ta musanta zargin, tana mai cewa kyaututtukan da aka ba ta ba cin hanci ba ne, yayin da lauyoyinta suka ce za su ɗaukaka ƙara.

Kotun ta gano cewa ta karɓi kayan ado da darajarsu ta haura won miliyan 100 daga wani shugaban kamfani domin taimaka wa ɗan surukinsa samun aikin gwamnati. Haka kuma an ce wani malami ya ba ta jaka ta alfarma ta Dior da wasu kyaututtuka domin neman taimako kan wasu al’amuran gwamnati.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yanke mata hukunci a gidan yari, bayan an same ta da laifin badakalar kasuwancin hannayen jari da kuma karɓar cin hanci daga wata ƙungiya.

Shi ma tsohon mijinta, tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol, yana gidan yari bayan an yanke masa hukuncin rai da rai kan zarge-zargen da suka shafi aika jirage marasa matuƙa zuwa Koriya ta Arewa da kuma yunƙurin kafa dokar ta baci a shekarar 2024.

Lamarin da yasa aka tsige Yoon daga mulki a shekarar 2025 ta hanyar tsarin dokar ƙasa.

0 $type={blogger}: