Kotun Kolin Isra’ila Ta Umarci A Ba Red Cross Damar Ziyartar Fursunonin Falasdinawa dake gidajen yarin ƙasar.

Kotun Kolin Isra’ila Ta Umarci A Ba Red Cross Damar Ziyartar Fursunonin Falasdinawa dake gidajen yarin ƙasar.

Kotun Kolin Isra’ila ta yanke hukuncin cewa gwamnati dole ne ta bai wa wakilan kungiyar agaji ta kasa da kasa, wato International Committee of the Red Cross (ICRC), damar ziyartar Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin kasar.

Kotun ta yi watsi baki daya da manufar gwamnatin da ta hana kungiyar Red Cross ziyartar fursunonin Falasdinawa tun bayan harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

A hukuncin da aka yanke ranar Laraba, alkalan kotun sun bayyana cewa hana kungiyar Red Cross ziyartar fursunoni ya saba wa dokokin Isra’ila da kuma dokokin kasa da kasa, don haka dole ne a soke wannan mataki.

Kotun ta kuma ce gwamnati ba ta gabatar da wata hujjar doka da za ta tabbatar da matakin dakatar da duk wata ziyara ga fursunonin bayan harin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum 1,100 tare da kama sama da mutum 240 a matsayin garkuwa.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Isra’ila, Association for Civil Rights in Israel (ACRI), wacce ta kai karar kotu, ta ce wannan ne karo na farko cikin shekaru 50 da Isra’ila ta hana Red Cross shiga gidajen yari domin ziyartar fursunoni.

ACRI ta bayyana cewa sama da fursunonin Falasdinawa 9,000 da ake tsare da su a gidajen yari da cibiyoyin tsarewa na soji za su sake samun damar ganawa da wakilan Red Cross bayan kusan shekaru uku ba tare da irin wannan ziyara ba.

A martaninta, kungiyar ICRC ta yi maraba da hukuncin kotun, tana mai cewa ta shirya komawa gudanar da ayyukanta na ziyartar wadanda ake tsare da su da zarar an kammala shirye-shiryen da suka dace tare da hukumomin Isra’ila.

Hukuncin ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan zarge-zargen cin zarafi da ake yi wa fursunonin Falasdinawa a gidajen yarin Isra’ila. 
Wani rahoto na United Nations ya ambaci zarge-zargen azabtarwa da fyade da tilasta tsiraici da wasu nau’o’in cin zarafi da aka ce sun faru a wasu cibiyoyin tsarewa na Isra’ila.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam sun bayyana hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da bin dokokin kasa da kasa da kuma kare hakkin fursunoni.

0 $type={blogger}: