Kamfanin kera kwakwalwan kwamfuta na Koriya ta Kudu, SK Hynix, ya zarce na Samsung Electronics wajen zama kamfanin da ya fi kowane daraja a kasuwar hannayen jari ta ƙasar, lamarin da ya nuna babban sauyi ga kamfanin da kusan ya durƙushe shekaru 20 da suka gabata saboda yawan basussuka.
Darajar SK Hynix ta ƙaru sosai a ranar Litinin sakamakon bunƙasar fasahar na’ura mai ƙirƙira (AI) a duniya, inda kamfanin ya zama ɗaya daga cikin manyan masu samar da kwakwalwan HBM (High Bandwidth Memory) da ake amfani da su a manyan tsarin AI.
Farashin hannayen jarin SK Hynix ya ƙaru da kashi 5.6 cikin 100, inda darajar kamfanin ya kai kusan tiriliyan 2,080.4 na won, ya zarce Samsung Electronics wadda darajarsa ya kai tiriliyan 2,066.7 na won.
Nasarar SK Hynix ya samo asali ne daga yawan buƙatar kwakwalwan HBM da ake amfani da su wajen gudanar da fasahohin AI na kamfanoni irin su Nvidia da Google.
Ci gaban AI ya sauya masana’antar kwakwalwan kwamfuta ta duniya, inda ƙananan kwakwalwan suka zama muhimman abubuwa wajen gina manyan tsarin fasahar zamani.
SK Hynix ya fi mayar da hankali wajen kera ƙwaƙwalwa kwamfuta, yayin da Samsung ke kuma kera wayoyi da talabijin da sauran kayayyakin lantarki.
Samsung ne ke riƙe da matsayin kamfani mafi daraja a Koriya ta Kudu tun shekara ta 2000.
Masana sun ce shawarar SK Hynix na ci gaba da saka jari a fasahar HBM a lokacin da masana’antar kwakwalwan kwamfuta ke cikin matsala ya taimaka masa wajen zama jagora a kasuwar duniya.
A shekarar 2025, SK Hynix ya mallaki kashi 61 cikin 100 na kasuwar HBM ta duniya, yayin da Samsung ke da kashi 17 cikin 100, Micron kuma keda kashi 21 cikin 100.
Kamfanin wanda aka kafa a shekarar 1983 a matsayin wani sashe na Hyundai, daga baya ya koma ƙarƙashin rukunin kamfanonin SK, Ya shawo kan matsalar kuɗi mai tsanani a farkon shekarun 2000, sannan ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin kwakwalwan kwamfuta a duniya.
A shekarar 2023, kamfanin ya fuskanci asara saboda faɗuwar farashin kwakwalwan kwamfuta, amma ya farfaɗo yayin da buƙatar AI ta ƙaru, inda ya samu riba mai tarihi a shekarar 2024.
Masana sun ce ci gaban SK Hynix na iya fara barazana ga matsayin Samsung a matsayin mafi girman mai kera DRAM a duniya a shekaru masu zuwa.
Rahotanni sun ce SK Hynix na shirin shiga kasuwar hannayen jari ta Amurka Nasdaq, matakin da zai iya ƙara yawan masu zuba jari daga ƙasashen waje.

0 $type={blogger}:
Post a Comment