Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yankewa tsohon Ministan Shari’a, Park Sung-jae, hukuncin shekaru 25 a gidan yari bisa zarginsa da hannu a rikicin dokar soji da tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol ya ayyana a shekarar 2024.
Kotun Gundumar Seoul ta Tsakiya ta same shi da laifin shiga cikin wani shiri na “tawayen mulki”, inda masu gabatar da ƙara suka ce ya goyi bayan matakan da suka yi barazanar karya tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Tsohon shugaban ƙasar Yoon ya ayyana dokar soji a cikin daren Disamba 2024, amma ta ɗauki kusan sa’o’i shida kacal bayan ‘yan majalisa sun yi gaggawar soke ta a zaman gaggawa.
Daga baya aka samu Yoon da laifin jagorantar tawaye, kuma a yanzu yana tsare yayin da yake ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa na daurin rai da rai.
Kotun ta ce Park, wanda shi ne Ministan Shari’a a lokacin, ya gudanar da taro da jami’an ma’aikatar bayan ayyana dokar sojin, tare da duba yiwuwar samun wuraren tsare mutane idan aka kama masu adawa da gwamnati.
Alƙali Lee Jin-gwan ya ce ayyukan Park sun kusa jefa ƙasar cikin yanayin da za a iya take haƙƙin jama’a da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
Masu gabatar da ƙara sun nemi a yanke masa hukuncin shekaru 20, suna zarginsa da yin amfani da matsayinsa wajen taimakawa shirin ayyana dokar soji.
Wasu tsoffin jami’an gwamnati da ke da alaƙa da lamarin su ma sun fuskanci hukunci, ciki har da tsohon Firayim Minista Han Duck-soo da aka yankewa shekaru 15 a gidan yari, da tsohon Ministan Cikin Gida Lee Sang-min da aka ba shekaru tara.
Tsohon Ministan Tsaro Kim Yong-hyun kuma an yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari bisa tona bayanan sirrin soji da suka shafi lamarin.
A gefe guda kuma, matar tsohon shugaban ƙasa, Kim Keon Hee, tana zaman gidan yari na shekaru huɗu bisa wasu tuhume-tuhume daban na magudin hannayen jari da cin hanci.

0 $type={blogger}:
Post a Comment