Hare-haren da Sojojin Amurka Suka Kai Najeriya Ya Dakatar da Kisan Kiristocin da akeyi a Ƙasar, Inji Donald Trump.

Hare-haren da Sojojin Amurka Suka Kai Najeriya Ya Dakatar da Kisan Kiristocin da akeyi a Ƙasar, Inji Donald Trump.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai kwanakin baya a Najeriya sun taimaka wajen dakatar da hare-haren da ake kai wa Kiristoci a kasar.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taro a Washington, inda ya ce harin sojin ya “rage sosai” abin da ya kira kashe-kashen al’ummar Kiristoci a Najeriya.

> “Ana yanka su… dubban mutane ne ake kashewa, ciki har da yara da mata da tsofaffi,” in ji Trump.

Ya yi ikirarin cewa matakin sojin ya hana ci gaba da kai hare-haren ta’addanci, yana mai cewa dakarun Amurka sun kai hari kan manyan shugabannin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

“Mun kashe shugabansu, na biyu da na uku,” in ji shi.

Trump ya kwatanta aikin da aka yi a Najeriya da ayyukan sojin Amurka a Iran, yana mai cewa Amurka za ta ci gaba da daukar mataki kan barazanar da take ganin yana da hatsari.

Ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kare Kiristoci da ’yancin addini a fadin duniya.

“Na ceto Kiristoci a duniya ta hanyar kai hari mai tsanani kan ’yan ta’adda,” in ji Trump.

A baya, sojojin Najeriya da Amurka sun gudanar da hare-haren sama kan mayakan ISIS da ISWAP a wasu sassan arewacin Najeriya. Hukumomin sojin Najeriya sun sanar cewa an kashe wasu mayaka da dama a hare-haren hadin gwiwa da aka kai a Jihar Borno.

0 $type={blogger}: