Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan alawus da tallafin kuɗi ga mambobin shirin bautar ƙasa na NYSC da ke aiki a jihar.
Wannan matakin na zuwa ne domin inganta walwala da jin daɗin masu bautar ƙasa da ke bayar da gudummawa wajen bunƙasa fannoni daban-daban a Zamfara.
A cewar sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, amincewar ta shafi masu bautar ƙasar na NYSC daga rukuni na Batch A Stream I da II har zuwa Batch C Stream I da II.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa wannan mataki ya nuna yadda take yabawa da kuma gane irin ƙoƙari, kishin ƙasa da sadaukarwar da matasan da suka kammala karatu suke yi a fannonin ilimi, lafiya, noma da sauran muhimman wurare.
Gwamna Lawal ya umarci ofishin Babban Akanta Janar na jihar da ya shirya dukkan hanyoyin da suka dace domin tabbatar da fara biyan kuɗin cikin sauƙi da bin ƙa’idojin da aka tanada.
Gwamnatin Zamfara ta gode wa mambobin NYSC bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma da kuma zaɓar yin hidima a jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment