Magidanta a sassa daban-daban na Najeriya sun fara samun sauƙi, yayin da farashin iskar gas ɗin girki (LPG) ya fara raguwa sakamakon ƙaruwa da ake samu wajen samar da shi da kuma sauƙin farashin wuraren ajiya.
Rahotannin kasuwa sun nuna cewa farashin gas ɗin girki ya fara sauka a manyan biranen ƙasar, duk da cewa saukar farashin bai yi daidai ba saboda bambancin kuɗin sufuri da nisan wuraren ajiya da kuma ribar masu sayarwa.
A Legas da Ibadan da Abeokuta, ana sayar da kilogram ɗaya na gas tsakanin Naira 1,100 zuwa Naira 1,350, yayin da a Benin City da Fatakwal da Warri farashin yake tsakanin Naira 1,150 zuwa Naira 1,400 kan kilo ɗaya.
A Onitsha da Enugu kuwa, farashin yana tsakanin Naira 1,200 zuwa Naira 1,450, yayin da a Abuja ake sayar da shi tsakanin Naira 1,250 zuwa Naira 1,500 kan kilo ɗaya.
Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Gas na LPG ta Najeriya, Edu Inyang, ya ce biranen arewa kamar Kano da Kaduna suna da farashi tsakanin Naira 1,300 zuwa Naira 1,550 kan kilo ɗaya, yayin da Maiduguri da wasu sassan Arewa maso Gabas ke da farashi mafi tsada daga Naira 1,350 zuwa Naira 1,650, saboda tsadar sufuri.
Ya bayyana cewa gaba ɗaya farashin gas a faɗin ƙasar yanzu yana tsakanin Naira 1,100 zuwa Naira 1,650 kan kilo ɗaya, ko da yake wasu wurare suna iya yin sama saboda tsadar jigilar kaya.
An danganta raguwar farashin da ƙarin samun gas daga cikin gida da kuma shigo da shi daga ƙasashen waje da raguwar farashin wuraren ajiya, da kuma ƙaruwar gasa tsakanin masu sayar da gas.
Yanzu sake cika kwalbar gas mai nauyin kilo 5 yana tsakanin Naira 5,500 zuwa Naira 8,250, yayin da kwalbar kilo 12.5 take tsakanin Naira 13,750 zuwa Naira 20,625, gwargwadon wurin da ake siya.
Masu sana’ar gas sun ce ana samun daidaito a kasuwar, amma sun yi gargadin cewa farashin na iya bambanta daga wuri zuwa wuri saboda kuɗin sufuri.
A baya, farashin gas ya tashi sosai daga kusan Naira 1,000 kan kilo ɗaya a farkon shekara zuwa kusan Naira 2,400 tsakanin watan Mayu da Yuni sakamakon ƙarancin samuwa.
Gwamnatin Tarayya daga baya ta shiga lamarin, inda ta gargaɗi masu sayar da gas kan boye kaya da ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment