Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa wasu ’yan takarar gwamna sun kashe tsakanin Naira biliyan 20 zuwa biliyan 30 domin samun tikitin jam’iyyunsu a zabukan fidda gwani gabanin babban zaben shekarar 2027.
Olukoyede ya yi wannan bayani ne a wani taron ilimi da “Cibiyar Nazari kan Zaman Lafiya da Tsare-tsaren Dabaru” ta shirya a Ilorin, inda ya gargadi cewa yawan kudaden da ake kashewa wajen neman mukaman siyasa na kara haddasa cin hanci da rashawa tare da barazana ga dimokuradiyya.
Ya ce idan ’yan siyasa suka kashe makudan kudade wajen lashe zabe, akwai yiwuwar su nemi dawo da kudaden da suka kashe ta hanyar karkatar da kudaden gwamnati bayan sun hau mulki.
A cewarsa, sayen kuri’u da amfani da kudi wajen tasiri kan masu zabe na raunana tsarin shugabanci nagari, domin masu cin zaben da irin wannan hanya kan fi mayar da hankali wajen dawo da jarin da suka kashe maimakon yi wa al’umma hidima.
Shugaban EFCC ya bayyana cewa hukumar ta kara kaimi wajen yaki da sayen kuri’u da sauran laifukan zabe, inda ya ce an kama mutane da dama tare da samun hukuncin kotu kan wasu da aka samu da hannu a irin wadannan laifuffuka.
Ya kuma jaddada cewa ba za a lamunci rashin hukunta masu karya dokokin zabe ba, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga dimokuradiyya da zaman lafiyar kasa.
Olukoyede ya kara da cewa EFCC na shirin amfani da jirage marasa matuki (drones) da sauran fasahohin zamani domin sa ido kan rumfunan zabe da kuma gano masu sayen kuri’u a zaben 2027.
Har ila yau, ya bukaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su mayar da hankali kan yakin neman zabe bisa manufofi da shirye-shirye, tare da kauce wa kalaman tunzura jama’a da ka iya haddasa tashin hankali.
Ya kuma yi kira ga hukumar zabe ta kasa, INEC da hukumomin tsaro da kungiyoyin farar hula da kafafen yada labarai su hada kai wajen tabbatar da gudanar da zabuka cikin lumana da adalci da gaskiya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment