Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wasu kadarori da suka haɗa da ofisoshi da shaguna a kan titin Murtala Mohammed, a yankin ƙaramar hukumar Fagge, jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne a kusa da wata ma’ajiyar kayan sifa da ake kira Kasuwar Takumbo, kafin daga bisani ta bazu zuwa wasu gine-gine da ke makwabtaka da wurin, ciki har da wuraren kasuwanci da ke kusa da reshen bankin First City Monument Bank.
A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, an samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 10:54 na dare, inda aka tura jami’an kashe gobara daga hedikwata da sauran tashoshin cikin birni zuwa wurin da lamarin ya faru.
Da isarsu, jami’an sun tarar da ginin bene mai hawa ɗaya da wasu sassan kasuwanci masu girman kusan mita 300 da 200 suna ci da wuta sosai. Sun yi kokarin shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu wurare.
Binciken farko ya nuna cewa gobarar ta fara ne daga ma’ajiyar kayan sifa, inda aka ajiye kayayyaki da dama kafin ta bazu zuwa gine-ginen da ke kusa.
An bayyana cewa bene na sama na ginin Kanawa ya kone, inda ofisoshi biyu da faloli biyu da bandakuna biyu da kicin suka lalace.
Haka kuma, gobarar ta lalata wasu shaguna biyu a ƙasan ginin TUSRAYS Nigeria Limited.
Hukumomi sun ce gobarar ta tashi ne sakamakon tashin wutar lantarki.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya shawarci mazauna da ’yan kasuwa su riƙa kula da harkokin tsaro na wuta, musamman wajen gyaran lantarki domin kauce wa irin wannan haɗari.
Ya kuma roƙi jama’a su riƙa sanar da hukumar kashe gobara da wuri idan gobara ta tashi, domin rage barna da kuma ceton rayuka da dukiyoyi.
Babu rahoton asarar rayuka a lokacin da aka fitar da wannan rahoto.

0 $type={blogger}:
Post a Comment