Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta zargi hukumomin Birtaniya da lalata mata suna da mutunci bayan wani bincike na tsawon shekaru 13 da ya kare da wanke ta daga zargin cin hanci.
A wata hira da BBC, Diezani mai shekaru 65 ta ce binciken da Hukumar Yaki da Laifuka ta Birtaniya (NCA) ta gudanar ya janyo mata wahala da damuwa sosai, kuma da an iya gudanar da shi ta wata hanya daban.
Ta ce binciken ya hana ta yin tafiye-tafiye da kuma aiki, sannan ya jawo mata tabarbarewar suna a idon jama’a.
Wata kotu a Birtaniya ta same ta ba ta da laifi kan tuhume-tuhume biyar da suka shafi karbar cin hanci da hada baki wajen aikata cin hanci, bayan shari’ar da aka fara a shekarar 2023.
Diezani, wadda ta rike mukamin Ministar Man Fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015 kuma ta kasance mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta duniya (OPEC), ta dage cewa ba ta aikata laifi ba.
An kama ta a shekarar 2015, amma ba a gurfanar da ita a gaban kotu ba sai shekarar 2023, inda ake zarginta da karbar alfarma daga wasu ‘yan kasuwar mai.
Lauyoyinta sun ce wasu muhimman takardu da za su iya taimaka wajen kare ta sun bace a Najeriya.
Tsohuwar ministar ta ce akwai bangarori da dama da ya kamata a duba alhakin da ya rataya a kansu, tare da yin kira da a sake nazarin yadda ake tafiyar da irin wadannan shari’o’i.

0 $type={blogger}:
Post a Comment