Kungiyar kwallon kafa ta Ƙasar Morocco ta doke Scotland da ci 1-0 a wasan rukuni na C na gasar cin kofin duniya na 2026.
Ismael Saibari ne ya jefa kwallon farko bayan dakika 71 kacal da fara wasan, inda ya kafa tarihin cin kwallo mafi sauri a gasar ta bana.
Wannan kwallon ce ta ba Morocco damar samun nasara a wasan da aka buga a filin wasa na Boston dake Amurka, yayin da Scotland ta yi kokarin samun damar rama kwallo amma ba ta yi nasara ba.
Da wannan nasarar, Morocco ta samu maki hudu daga wasanni biyu, kuma tana dab da tsallakawa zuwa zagayen gaba na gasar.
Scotland kuwa ta samu matsala wajen kirkirar damammaki masu kyau, kuma yanzu za ta kara da Brazil a wasanta na gaba domin neman damar ci gaba a gasar.
Morocco za ta kara da Haiti a wasanta na gaba a rukunin C.

0 $type={blogger}:
Post a Comment