Cutar kwalara ta tsananta a jihar Borno, yayin da ta yadu zuwa jihar Filato.

Cutar kwalara ta tsananta a jihar Borno, yayin da ta yadu zuwa jihar Filato.

Najeriya na fuskantar barazanar sake bullar cutar kwalara yayin da ake shiga tsakiyar damina, inda aka samu barkewar cutar a jihohin Borno da Filato.

Hukumomin lafiya sun ce cutar da ake kamuwa da ita ta hanyar gurbataccen ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da kamuwa da dubban wasu. 
An danganta karuwar cutar da rashin tsaftataccen ruwa da matsalar tsafta da yawan kauracewar jama’a da kuma raunin tsarin kiwon lafiyar jama’a.

A jihar Borno, lamarin ya zama daya daga cikin manyan matsalolin kwalara da aka taba gani a ‘yan shekarun nan. Bayanan kungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) sun nuna cewa jihar ta samu mutuwar mutane 35 da kuma sabbin kamuwa da cutar su 3,646 cikin mako guda.

Tsakanin farkon watan Mayu zuwa ranar 9 ga Yuni, an samu rahoton mutuwar mutane 74 da kuma mutane 7,850 da ake zargi sun kamu da cutar a kananan hukumomi 12 na jihar.

Birnin Maiduguri ne ya fi fama da matsalar, inda aka samu fiye da rabin adadin wadanda suka kamu.

A sansanin ‘yan gudun hijira da ke Monguno, ta jihar Borno, an samu mutane 296 da ake zargi sun kamu da cutar cikin kwanaki uku kacal.

Ma’aikatan lafiya sun ce yawan masu zuwa cibiyoyin jinya na kwalara ya kara matsin lamba kan kayan aiki da ma’aikata.

Bayanan sun nuna cewa an samu mutane 48 a ranar 11 ga Yuni da 68 a ranar 12 ga Yuni sannan 180 a ranar 13 ga Yuni.

Mafi yawan wadanda suka kamu mata ne da yara daga sansanonin ‘yan gudun hijira. Jami’an lafiya sun yi gargadin cewa wasu mutane suna jinkirta zuwa asibiti, lamarin da ya jawo wasu rasuwa a gidajensu.


Jihar Filato ma ta tabbatar da bullar cutar kwalara a karamar hukumar Mangu.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Nicholas Baamlong, ya ce mutane biyar sun mutu, yayin da aka samu mutane 52 da ake zargi sun kamu da cutar, kuma 11 suna samun magani a asibitoci.

An samu matsalar a yankunan Pushit da Mangu I da Mangu II.

Dalilan Da Suka Jawo Bullar Cutar

Masana kiwon lafiyar jama’a sun ce bullar kwalara ba abin mamaki ba ne, saboda matsalolin tsafta da rashin samun ingantaccen ruwa.

Sun bayyana cewa cutar tana yaduwa cikin sauri a wuraren da jama’a ke amfani da ruwa mara tsafta da rashin bandaki da kuma cunkoson jama’a.

Masana sun ce matsalar rikici da gudun hijira a Borno ta kara jefa jama’a cikin hadari, saboda mutane da dama suna rayuwa a wuraren da ba su da isasshen ruwa da kayan tsafta.

Sun kuma yi gargadin cewa ambaliyar ruwa a lokacin damina na iya kara gurbata hanyoyin samun ruwa.

Jihohi Sun Kara Shirye-shiryen Dakile Cutar

Jihohi da dama a Arewacin Najeriya sun kara sanya ido tare da daukar matakan dakile yaduwar cutar.

Jihar Benuwe ta ce ta kafa kungiyoyin gaggawa, ta kara wayar da kan jama’a tare da tanadar kayan magani.

Jihohin Taraba da Bauchi da Kebbi sun ce suna kara sa ido da shirye-shiryen kariya duk da cewa ba su samu manyan bullar cutar ba.

Hukumomin lafiya sun bukaci jama’a su kula da tsafta, su sha ruwa mai tsafta, sannan su garzaya asibiti idan suka ga alamun cutar kamar gudawa mai tsanani da amai.

0 $type={blogger}: