Ƙasar Ireland Ta Kori Mutane 42 Ɗan asalin Afirka ta Kudu, Ciki Har da Yara 15 saboda dalilan aikata laifuka.

Ƙasar Ireland Ta Kori Mutane 42 Ɗan asalin Afirka ta Kudu, Ciki Har da Yara 15 saboda dalilan aikata laifuka.

Hukumomin ƙasar Ireland sun kori ’yan ƙasar Afirka ta Kudu 42 daga ƙasar, ciki har da yara 15, kamar yadda Ministan Shari’a na Ireland, Jim O’Callaghan, ya bayyana.

Mutanen da aka kora — maza tara, mata 18 da ƙananan yara 15 daga wasu iyalai — sun isa Johannesburg a safiyar Alhamis bayan an ɗauke su daga Dublin da jirgin haya na musamman.

Biyu daga cikin mutanen da aka kora an taɓa samun hukuncin laifi a kansu a Ireland.

Ofishin kula da shige da fice na ’yan sanda na Ireland (Garda National Immigration Bureau) ne ya gudanar da aikin korar, bisa umarnin kora da Ministan Shari’a ya bayar.

Wannan shi ne karo na huɗu da Ireland ta gudanar da jirgin korar baƙi a wannan shekarar. Ma’aikatar Shari’a ta ce kawo yanzu an kori mutane 130 daga ƙasar, ciki har da ’yan ƙasashen Tarayyar Turai 67 saboda dalilan aikata laifuka.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa kuɗin wannan jirgin korar ya kai Euro 735,000.

Ministan Shari’a O’Callaghan ya ce umarnin kora na da muhimmanci domin tabbatar da tsarin shige da fice na Ireland yana aiki yadda ya kamata.

0 $type={blogger}: