Ƙasar Faransa ta ce ba za a cire takunkuman majalisar ɗinkin duniya kan Iran ba sai da yardarta.

Ƙasar Faransa ta ce ba za a cire takunkuman majalisar ɗinkin duniya kan Iran ba sai da yardarta.

Ƙasar Faransa ta bayyana cewa ba za ta amince da cire takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya da aka kakabawa Ƙasar Iran ba, sai idan ta gamsu da sharuɗɗan yarjejeniyar ƙarshe kan shirin nukiliyar Iran.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noël Barrot, ya ce dole ne Faransa ta kasance cikin tattaunawar da ta shafi Iran, kasancewar tana cikin ƙasashen da ke da kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya tare da ikon amfani da veto.

Barrot ya bayyana cewa babu yiwuwar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya matuƙar tattaunawar Amurka da Iran ba ta shafi shirin makaman roka masu linzami na Iran da kuma goyon bayan da take bai wa wasu ƙungiyoyi a yankin ba.

Ya ce duk wata yarjejeniya da za ta haifar da rangwame daga Iran za ta kasance tare da batun cire takunkuman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kakaba mata.

Faransa da Birtaniya da Jamus sun nemi a basu damar shiga tattaunawar da za a yi nan gaba, saboda fargabar cewa tattaunawar da Amurka ke jagoranta ba za ta magance dukkan matsalolin shirin nukiliya da makamai masu linzami na Iran ba.

Kasashen uku na Turai sun taba yin aiki tare da Iran da Amurka wajen cimma yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015, wadda ta bai wa Iran damar samun sassaucin takunkumi bisa sharadin rage ayyukan nukiliyarta.

Ministan Faransa ya ƙara da cewa ƙasarsa za ta taka rawa wajen warware rikicin saboda matsayinta a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

0 $type={blogger}: