Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ghana ta samu nasara mai ban mamaki bayan ta doke Panama da ci 1-0 a wasan farko na su a gasar cin kofin duniya ta 2026 da aka buga a birnin Toronto.
Dan wasan Ghana, Caleb Yirenkyi ne ya zura ƙwallon da ta ba ƙasar nasara a minti na biyar na ƙarin lokaci bayan kammala mintuna 90. Brandon Thomas-Asante ne ya fara kai harin gaggawa sannan ya miƙa ƙwallon zuwa tsakiyar fili inda Yirenkyi ya tura ta cikin raga.
Bayan Ghana ta ci ƙwallon, an samu hayaniya tsakanin 'yan wasa daga bangarorin biyu kafin alkalin wasa ya busa ƙararrawar kammala wasa.
Wasan ya kasance muhimmi ne ga ƙasashen biyu da ake ganin za su fafata domin samun matsayi na uku a rukunin L. Panama ce ta fi ƙarfi a farkon rabin wasan, amma Ghana ta dawo da ƙarfi a rabin na biyu.
Mai tsaron ragar Ghana, Lawrence Ati Zigi, ya yi wasu muhimman ceto a farkon wasan, sai dai an sauya shi a hutun rabin lokaci saboda rauni.
Ghana ba ta yi farmaki ko guda a ragar Panama a farkon rabin wasan ba, amma ta inganta wasanta bayan hutun rabin lokaci, inda har ta samu damar cin ƙwallon da ya bata nasara.
Wannan ita ce karo na biyar da Ghana ke halartar gasar cin kofin duniya cikin gasar shida da suka gabata. Mafi kyawun sakamakonta shi ne lokacin da takai matakin kusa da ƙarshe a shekarar 2010.
Panama, wadda wannan shi ne karo na biyu da take buga gasar, za ta nemi farfaɗowa a wasanta na gaba da Croatia.
Ghana za ta kara da Ingila a wasa na gaba, yayin da Panama za ta fafata da Croatia.

0 $type={blogger}:
Post a Comment