An Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Osun

An Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Osun

Wasu ‘yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Ifedayo da ke Jihar Osun, Mista Debo Farounbi, bayan sun kai hari garin Ora da ke kan iyakar jihohin Osun da Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Talata, lokacin da maharan suka shiga garin suna harbe-harbe a iska, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

An ce Farounbi da wasu mutum uku ne aka fara yin garkuwa da su. Sai dai jami’an tsaro da sojoji tare da masu sa-kai na yankin sun yi gagarumar fafatawa da maharan, lamarin da ya sa suka saki mutum uku daga cikin wadanda suka kama.

Duk da haka, maharan sun tsere da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar bayan musayar wuta mai tsanani.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun riga sun nufi dajin da wadanda suka sace kafin jami’an tsaron su kai dauki.

Ya ce, “Mutane hudu aka sace, ciki har da mata Fulani biyu da maza biyu. Saboda matsin lambar da sojoji suka yi, maharan sun bar mutum uku, amma sun gudu da Debo Farounbi.”

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an tsaro sun gaggauta kai dauki bayan harin, kuma ana ci gaba da kokarin ceto wanda aka sace.

“Mutum daya ne har yanzu ke hannun masu garkuwan, kuma shi ne Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar. Sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa, kuma ana ci gaba da kokarin kubutar da shi,” in ji Ojelabi.

Wannan shi ne karo na uku da ake samun irin wannan harin satar mutane a garin Ora cikin watanni bakwai da suka gabata.

A watan Disamban 2025, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani jami’in Kwastam mai ritaya mai suna Emmanuel Owolabi. 
Daga bisani an sake shi bayan ya shafe kusan makonni hudu a hannun masu garkuwan.

Haka kuma, a watan Fabrairun 2026, wasu maharan sun sake sace mazauna yankin biyu, wadanda daga baya aka sake su bayan kusan wata guda a tsare.

Mazauna yankin sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kara yawan jami’an tsaro a yankin domin dakile yawaitar hare-haren satar mutane.

Wata shugabar kasuwa da aka bayyana da sunan Misis Alarape ta ce mutane da dama sun fara barin garin saboda rashin tsaro.

Ta ce, “Mutane suna ci gaba da ficewa daga garin. Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, karin mutane za su bar yankin. 
Yawancin maharan suna shigowa ne ta bangaren iyakar Jihar Kwara.”

Jami’an tsaro sun ce suna ci gaba da kokarin gano maboyar masu garkuwa da mutanen tare da kubutar da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar cikin koshin lafiya.

0 $type={blogger}: