Wani mazaunin kauyen Guradnayi da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, Victor Solomon, ya bayyana yadda harin jirgin sama ya kashe masa ’ya’yansa uku tare da jikkata shi sosai.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da jiragen sojoji suka kai hari kan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da suke wucewa ta kauyukan da ke kusa da Kusasu a Shiroro.
Mazauna yankin sun ce fararen hula da dama, musamman yara kanana, sun mutu sakamakon harin.
Da yake magana daga gadon asibiti, Solomon ya ce ya samu munanan raunuka a fuska kuma yana cikin matsanancin hali.
“Na rasa ’ya’yana uku a harin. Ina cikin tsananin ciwo kuma muna bukatar taimakon gwamnati,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Gideon Bamaiyi, ya ce mutum 13 sun mutu a gidan babban yayansa bayan wani bam ya fada gidan yayin da mutane ke barci.
Ya ce daga cikin wadanda suka mutu akwai yara bakwai, yayin da wasu mutum shida ke karbar magani a wani asibiti da ke Zumba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa tun farko wasu ’yan bindiga ne suka bi ta yankin kafin harin ya faru, lamarin da ya sa mutane da yawa suka tsere daga gidajensu. Sai dai wasu sun dawo gida kafin harin ya faru da misalin karfe 5 na safe.
Sai dai Rundunar tsaron Najeriya ta musanta rahotannin cewa fararen hula sun mutu a harin.
Daraktan yada labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce sojoji sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri cewa ’yan bindiga sun taru a Shiroro.
A cewar rundunar sojin, an kai hare-hare ta sama a maboyar ’yan bindiga da ke Kusasu da Katerma da Bokko da Kuduru, inda aka kashe kusan ’yan bindiga 70.
Sojojin sun dage cewa harin ya yi daidai da wuraren da aka nufa kuma an gudanar da shi ne bisa sahihan bayanan sirri. Sun kuma ce an gargadi mazauna yankunan su fice kafin a fara aikin.
Haka kuma gwamnatin jihar Neja ta ce mutanen da suka rage a wuraren da aka kai harin su ne ’yan ta’adda da masu ba su bayanai.
Lamarin ya sake tayar da hankula kan hare-haren kuskure da jiragen soji ke yi a Najeriya, bayan makamantan hare-hare da suka taba faruwa a jihohin Borno da Kaduna da Zamfara da sauran sassan kasar nan.
Source: Dailytrust


0 $type={blogger}:
Post a Comment