Ƙasar Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutumin da aka kama da yi wa hukumomin leken asirin Amurka da Israi'la aiki.

Ƙasar Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutumin da aka kama da yi wa hukumomin leken asirin Amurka da Israi'la aiki.

Mahukuntan kasar Iran sun sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin yi wa hukumar leken asirin Amurka ta CIA da kuma hukumar leken asirin Isra’ila ta Mossad aikin leken asiri.

Rahotanni daga bangaren shari’ar Iran sun bayyana cewa mutumin, mai suna Erfan Shakourzadeh, ya kasance yana aiki da wata cibiyar fasahar tauraron dan adam a Iran kafin daga bisani ya shiga hulda da jami’an leken asirin kasashen waje.

A cewar hukumomi, bincike ya nuna cewa wanda aka yankewa hukuncin ya mika wasu muhimman bayanai ga Mossad tare da neman kulla alaka da CIA domin samun damar shiga Amurka da ci gaba da karatu a can.

Rahoton ya ce an tuntube shi ne ta kafar LinkedIn daga wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin dan Iran mazaunin Canada, wanda daga baya aka gano cewa jami’in Mossad ne da ke fakewa.

Mahukuntan Iran sun ce an tabbatar da laifukan ne ta hanyar hujjoji da bayanan da wanda ake zargin ya amsa yayin gudanar da bincike da shari’a.

Kotun Koli ta Iran ta tabbatar da hukuncin bayan kammala dukkan matakan shari’a, kafin daga bisani a aiwatar da hukuncin kisan a safiyar Litinin.

Lamarin na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Iran da kasashen yamma, musamman Amurka da Isra’ila, ke ci gaba da kara tsananta.

0 $type={blogger}: