Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Zuwa Faransa da Kenya da Rwanda.

Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Zuwa Faransa da Kenya da Rwanda.

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Abuja ranar Asabar, 2 ga Mayu, domin wata muhimmiyar ziyara zuwa ƙasashen Faransa, Kenya da Rwanda, a wani yunƙuri na ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da bunƙasa tattalin arziki.

Sanarwar hakan ta fito ne daga mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, wanda ya bayyana cewa shugaban zai fara ne da ziyara a Faransa kafin ya wuce Nairobi, babban birnin Kenya.

A Nairobi, Shugaba Tinubu zai halarci taron Africa-France Summit, wanda shugabannin ƙasashen Emmanuel Macron na Faransa da William Ruto na Kenya za su jagoranta. Taron zai tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da sauyin makamashi, bunƙasa masana’antu masu kare muhalli, ci gaban fasaha, da magance matsalolin sauyin yanayi.

Ana sa ran shugaban zai halarci taron daga ranar 11 zuwa 12 ga Mayu, inda za a tattauna hanyoyin inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da bunƙasa matasa da fasaha a nahiyar Afirka.

Bayan kammala taron a Kenya, shugaban zai wuce Kigali a Rwanda domin halartar taron Africa CEO Forum daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu. Taron, wanda ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar International Finance Corporation, zai haɗa manyan ‘yan kasuwa da masu zuba jari sama da 2,000 domin tattauna hanyoyin bunƙasa kasuwanci da haɗin gwiwar tattalin arziki a Afirka.

A yayin wannan tafiya, Shugaba Tinubu zai gabatar da manufofin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa tare da jawo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya. Haka kuma zai gana da manyan shugabannin kasuwanci da na siyasa daga sassa daban-daban na duniya.

Za a raka shugaban da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala tarukan a Rwanda.

0 $type={blogger}: