Shugaban Amurka Donald Trump ya kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai Beijing bayan ganawa da Shugaban ƙasar China Xi Jinping kan batutuwa da suka haɗa da kasuwanci da makamashi da batun yankin Taiwan da tsaron yankuna.
Ziyarar ita ce ta farko da Trump ya kai China cikin kusan shekaru goma, inda aka gudanar da taruka da liyafar gwamnati tare da nuna gagarumar maraba tsakanin bangarorin biyu.
Kafofin yaɗa labaran gwamnatin China sun bayyana cewa shugabannin biyu sun amince da wani tsarin “zaman lafiya da daidaito” domin jagorantar dangantakar ƙasashen biyu na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Trump ya kuma ce China ta amince za ta ƙara sayen man fetur daga Amurka tare da kulla yarjejeniyar sayen jiragen sama 200 daga kamfanin Boeing.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta kuma shafi rikicin Iran da takaddamar kasuwanci da kuma batun yankin Taiwan.
Masana harkokin siyasa da tattalin arziki na ganin taron na Beijing zai iya yin tasiri ga kasuwannin duniya da farashin makamashi da kuma makomar dangantakar Amurka da China a nan gaba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment