Kwankwaso Ya Tsayar da Gwarzo a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano na Jam'iyyar NDC.

Kwankwaso Ya Tsayar da Gwarzo a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano na Jam'iyyar NDC.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress domin zaben shekarar 2027.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a bayan tuntubar shugabannin jam’iyyar.

Kwankwaso ya kuma sanar da cewa tsohon mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, zai tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya karkashin jam’iyyar NDC.

A cewarsa, an dauki matakin ne bisa adalci da kwarewa da biyayya da kuma kokarin tabbatar da hadin kai a cikin tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

“Ina farin cikin sanar da cewa Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo shi ne dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyarmu. Haka kuma Dr Nasiru Yusuf Gawuna zai yi takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya,” in ji Kwankwaso.

Ya kuma yi addu’ar samun nasara tare da gudanar da tsarin tabbatar da ‘yan takara cikin lumana.

Gwarzo ya taba rike mukamin mataimakin gwamna a gwamnatin Abba Kabir Yusuf kafin sauye-sauyen siyasa su haifar da ficewarsa daga mukamin. 
Haka kuma ya taba zama Kwamishinan Harkokin Jiha da kuma Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo.

A nasa bangaren, Gawuna, wanda ya kasance dan takarar gwamna a Jam'iyyar APC a zaben 2023, ya koma NDC bayan barin jam’iyyar APC tare da hada kai da Kwankwaso.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan mataki zai kara zafafa siyasar Kano yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027.

0 $type={blogger}: