Fiye da Iyalai 1,000 ne Suka Amfana da Shirin Ragin Farashin Ragunan Layya a jihar Legas.

Fiye da Iyalai 1,000 ne Suka Amfana da Shirin Ragin Farashin Ragunan Layya a jihar Legas.

Mazauna yankin Odi-Olowo/Ojuwoye LCDA a Jihar Legas sun amfana da shirin sayar da ragunan Sallah a farashi mai sauki domin taimakawa al’umma yayin bikin Eid-el-Kabir.

Shirin ya bai wa fiye da mutane 1,000 damar sayen raguna kan kudi N80,000 kacal, farashin da ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da yadda ake sayar da su a kasuwa, inda wasu ke kaiwa tsakanin N350,000 zuwa N400,000.

Shugaban yankin LCDA din, Seyi Jakande, ya ce an kirkiro shirin ne domin rage wa iyalai nauyin kashe kudade yayin bukukuwan Sallah tare da tallafawa masu karamin karfi.

A cewarsa, shirin wani bangare ne na kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar jama’a da bunkasa walwalar al’umma a matakin kasa.

Jakande ya bayyana cewa masu anfani da shirin dole ne su gabatar da katin zabe na dindindin ko na wucin gadi kafin su samu damar shiga cikin shirin, yana mai cewa hakan zai kara karfafa shiga harkokin zabe da dimokuradiyya.

Ya kara da cewa gwamnatin karamar hukumar na shirin ci gaba da gudanar da irin wannan tallafi duk shekara domin taimakawa al’umma da kara dankon zumunci tsakanin gwamnati da jama’a.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun yabawa shirin, suna masu cewa ya zo a daidai lokacin da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci ke ci gaba da addabar jama’a.

0 $type={blogger}: