Kotu a Abuja za ta saurari ƙarar da ke kalubalantar yiwuwar takarar Jonathan a zaɓen 2027.

Kotu a Abuja za ta saurari ƙarar da ke kalubalantar yiwuwar takarar Jonathan a zaɓen 2027.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja za ta saurari wata ƙara a yau da ke neman hana tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen shekarar 2027, a cikin sabon muhawarar doka kan iyakacin wa’adin mulki a kundin tsarin mulki.

An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025 ne daga wani lauya, Johnmary Jideobi, wanda ke neman kotu ta ayyana Jonathan a matsayin wanda bai cancanci sake tsayawa takara ba bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Mai shari’a Peter Lifu ya riga ya umarci a aike da sanarwar zaman kotu ga dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar, bayan wasu daga cikinsu sun gaza mika martaninsu a kan lokaci.

Jonathan shi ne wanda ake tuhuma na farko, yayin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kuma Antoni-Janar na Tarayya suke matsayin waɗanda ake tuhuma na biyu da na uku.

Mai shigar da ƙara na neman kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya a matsayin ɗan takara, tare da hana INEC karɓa ko wallafa sunansa a jerin ‘yan takara.

A cewar mai ƙarar, batun da ke gaban kotu shi ne ko Jonathan ya riga ya kammala wa’adin mulki biyu da kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya ce Jonathan ya fara jagorancin ƙasa ne a 2010 bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, sannan ya kammala wa’adin, daga bisani kuma ya ci gaba da mulki bayan lashe zaɓen 2011.

A cikin bayanin rantsuwa da aka gabatar a kotu, an ce sake takarar Jonathan a 2027 zai kai ga yin rantsuwar shugabanci karo na uku, wanda ake ganin ya sabawa doka.

Har ila yau, an bayyana cewa idan kotu ba ta dakile hakan ba, wata jam’iyya na iya tsayar da shi takara, abin da ka iya haifar da rikici kan bin doka da oda.

Wannan shari’a na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan yiwuwar dawowar Jonathan fagen siyasa, duk da cewa bai fito fili ya tabbatar da burin takara ba.

A baya-bayan nan, ya mayar da hankali kan batun inganta halartar zaɓe da kuma kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa, da su shiga harkar dimokuraɗiyya.

Ya kuma yi gargadi kan ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Najeriya, tare da jaddada bukatar shugabanni su tsara makomar ƙasa mai dorewa.

0 $type={blogger}: