Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba kyautar kuɗi Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin ₦450,000) ga kowanne mahajjacin jihar su 2,410 da ke aikin Hajjin 2026 a ƙasar Saudiyya.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba kyautar kuɗi Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin ₦450,000) ga kowanne mahajjacin jihar su 2,410 da ke aikin Hajjin 2026 a ƙasar Saudiyya.

An bayyana wannan ne a daren Alhamis a Mina ta hannun Amirul Hajj na jihar, Muhammad Mai Gari Dingyadi, wanda ya ce Gwamna Ahmed Aliyu ne ya amince da wannan tallafi domin taimaka wa mahajjatan yayin da suke kammala ibadarsu da kuma shirye-shiryen komawa Najeriya.

A cewarsa, wannan tallafi na kuɗi an yi shi ne domin rage wa mahajjata nauyin kashe kuɗi a kwanakin ƙarshe na zamansu a ƙasa mai tsarki da kuma tafiyar dawowa gida.

Ya yaba da kyakkyawan halayen mahajjatan Sokoto, inda ya ce sun bi dokokin Saudiyya kuma sun nuna ladabi da kame kai a duk tsawon lokacin aikin Hajji.

Dingyadi ya ce babu wani mahajjaci daga jihar da ya karya doka ko ya shiga matsala, yana mai kiran su a matsayin jakadu nagari na Jihar Sokoto.

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da tallafa wa jama’a, musamman masu aikin Hajji, tare da mayar da hankali kan inganta rayuwar al’umma.

A ƙarshe, ya yi kira ga mahajjatan da su ci gaba da yin addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya, tare da roƙon Allah ya taimaki gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu wajen gudanar da mulki cikin nasara.

0 $type={blogger}: