Dan Takarar APC, Mahmud Buba, Ya Janye Daga Takarar Majalisar Wakilai, Inda Ya Bukaci A Mara Wa Dan Takarar APC Baya.

Dan Takarar APC, Mahmud Buba, Ya Janye Daga Takarar Majalisar Wakilai, Inda Ya Bukaci A Mara Wa Dan Takarar APC Baya.

Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye daga takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Sabon Gari ta tarayya.

A cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna, Buba ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan kokarin sulhu da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka fara gudanarwa.

Ya ce matakin janyewar ba abu ne mai sauki ba, amma bayan tuntuba da iyalansa da abokan siyasarsa da shugabannin jam’iyya, ya fahimci cewa hakan shi ne mafi alheri ga jam’iyyar APC kafin babban zabe.

Buba ya bayyana cewa hadin kai da mara wa dan takarar da jam’iyya ta amince da shi baya na da muhimmanci wajen samun nasara a zabe da kuma cigaban mazaba da jihar Kaduna baki daya.

Dan siyasar ya kuma yabawa Uba Sani da shugabannin APC bisa damar da suka ba shi na shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kara da cewa janyewar tasa ba alamar gazawa ba ce, illa wata sadaukarwa ce domin karfafa jam’iyyar da tabbatar da nasararta a zabe mai zuwa.

Buba ya kuma bukaci magoya bayansa da su kasance cikin kwanciyar hankali tare da mara wa duk wanda ya zama dan takarar APC baya domin ci gaban jam’iyyar.

A baya dai dan takarar ya fuskanci ce-ce-ku-ce kan shekarunsa bayan wasu sun wallafa bayanan fasfo dinsa suna ikirarin cewa yana da shekara 16 kacal mai makon 30.

0 $type={blogger}: