Wani mummunan hatsarin sufuri ya faru a birnin Bangkok, inda akalla mutane takwas suka rasa rayukansu sannan wasu 25 suka jikkata bayan wani jirgin kasa mai daukar kaya yaci karo da motar bas a tsakiyar birnin.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da rana kusa da tashar layin jirgin kasa a tsakiyar Bangkok, lokacin da motar bas din ta makale a mashigar jirgin kasa yayin da shingen kariya ke rufewa.
Shaidun gani da ido sun ce jirgin ƙasan ya bugi motar bas din da ta tsaya, inda ya ja ta a kan layin dogo kafin ta kama da wuta.
Jami’an agajin gaggawa sun isa wajen da lamarin ya faru domin ceto wadanda suka makale tare da kashe gobarar, Yayin da aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa.
Hukumomi a Thailand har yanzu ba su tabbatar da ainihin musabbabin hatsarin ba, kuma ana ci gaba da bincike.
Hatsarin ya faru ne a wani yanki mai cunkoso a cikin birnin, lamarin da ya sake tayar da tambayoyi kan tsaron hanyoyin jiragen kasa da tsarin zirga-zirga a biirnin na Bangkok.

0 $type={blogger}:
Post a Comment