Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wata budurwa mai shekaru 19, ‘yar hamshakin wani dan kasuwa a Abuja, duk da cewa iyalanta sun biya kudin fansa har naira miliyan 12 domin a sake ta.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace budurwar tare da mahaifinta, Muhammad Shuaibu, a lokacin da maharan suka kai hari. Bayan tattaunawa, iyalan sun tara kudin fansa tare da biyan abin da aka nema, da fatan za a sako su cikin koshin lafiya.
Sai dai, duk da biyan kudin fansar, an ruwaito cewa maharan sun kashe yarinyar, lamarin da ya janyo bakin ciki da fusata a tsakanin al’umma, tare da kara nuna damuwa kan matsalar tsaro da yawaitar sace-sacen mutane a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wannan lamari ya sake bayyana irin hatsarin da ‘yan bindiga ke haifarwa, inda suke karbar kudin fansa amma ba sa cika alkawari, lamarin da ke barin iyalai cikin jimami da radadi.

0 Comments:
Post a Comment