Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Baga, da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda suka kashe aƙalla mutane biyar sannan suka sace kimanin mutane 150.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da makamai masu ƙarfi, Inda suka kona gidaje da dama.
Mutane da yawa sun tsere zuwa daji don tsira, amma wasu an harbe su, yayin da wasu aka tafi da su zuwa cikin daji.
Wasu ‘yan sa-kai da suka yi ƙoƙarin kare al’umma sun jikkata sakamakon harbin da ‘yan bindigar suka yi musu. Ana zargin maharan sun shigo ne daga jihar Kaduna mai makwabtaka, inda suka haddasa wannan ɓarna mai girma.
Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro, Ishyaku Bawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da jami’an tsaro suka tura ƙarin dakaru domin ceto waɗanda aka sace da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Lamarin na ƙara nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankunan arewacin Najeriya, musamman hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomi.

0 Comments:
Post a Comment