Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa rabon buhunan shinkafa da taliya ba zai taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samun nasara a zaben shugaban kasa na 2027 ba.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata a Abuja, Atiku ya jaddada cewa kayayyakin agaji na ɗan lokaci ba za su maye gurbin amincewar jama’a ba. Ya ce: “Buhunan shinkafa da taliya da Indomie na iya kawo sauƙi na ɗan lokaci, amma ba za su iya tabbatar da nasara a zaɓe ba.”
Har ila yau, Atiku ya nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin ɗaure iko da rage dimokuradiyya, tare da jan hankali cewa rinjayen jam’iyyar gwamnati bai haifar da gamsuwar jama’a ba. Ya yi gargadi cewa rikicin siyasa na iya kai Najeriya ga tsarin jam’iyya daya idan ba a bi hanyar dimokuradiyya da ‘yancin zaɓe ba.

0 Comments:
Post a Comment