Rasha ta Tabbatar da Mutuwar Sojojin Kamaru 16 a Yakin Ukraine.

Rasha ta Tabbatar da Mutuwar Sojojin Kamaru 16 a Yakin Ukraine.

Gwamnatin Rasha ta tabbatar da cewa akalla sojojin ƙasar Kamaru 16 ne suka mutu yayin da suke fafatawa a yakin da ake yi a Ukraine.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan sojoji na daga cikin waɗanda aka ɗauka aiki ko suka shiga rundunar Rasha domin taimakawa a yaƙin da ke gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Har yanzu dai ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka ɗauke su aiki ba, amma ana zargin wasu daga cikinsu sun shiga ne ta hanyar kwangila ko kuma wasu hanyoyin sirri.

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar Kamaru, inda jama’a da dama ke nuna damuwa kan yadda ‘yan ƙasar ke shiga rikice-rikicen ƙasashen waje.

Yaƙin tsakanin Rasha da Ukraine ya shafe fiye da shekaru biyu yana gudana, inda ya jawo asarar rayuka da dama da kuma barnar dukiya mai yawa.

Masana harkokin tsaro na gargadi cewa yawan shiga ‘yan ƙasashen waje cikin wannan yaƙi na iya ƙara rikita lamarin da kuma tsawaita rikicin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: