Akalla mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani kauye da ke jihar Adamawa.
Harin ya faru ne a ranar Lahadi a kauyen Guyaku, cikin karamar hukumar Gombi, inda rahotanni suka ce maharan sun kai harin ne kan matasa da suka taru a wani filin wasan kwallon kafa, lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa.
Gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da yawan wadanda suka mutu yayin da ya kai ziyara yankin, inda ya bayyana harin a matsayin abin takaici da tayar da hankali.
Rahotanni daga jami’ai da mazauna yankin sun nuna cewa:
Maharan sun shafe awanni da dama suna harbe-harbe, inda Suka kona gidaje da wuraren ibada tare da lalata dukiyoyi da kona babura da sauran kayayyaki.
Gwamnan ya danganta harin da kungiyar Boko Haram, wadda ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
Wannan hari na daga cikin matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya, musamman a Arewa, inda ake fama da hare-haren ‘yan ta’adda da ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na fili.

0 $type={blogger}:
Post a Comment