Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da nadin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na Murtala Sule Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamna.
A zaman majalisar da aka gudanar, ‘yan majalisa sun tattauna tare da amincewa da nadin bayan tantancewa, inda suka bayyana gamsuwa da cancantar sa.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sauyin da aka samu a fadar gwamnatin jihar, inda ake sa ran sabon mataimakin gwamnan zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban gwamnati da tafiyar da harkokin mulki.

0 $type={blogger}:
Post a Comment