Wani ɗan Najeriya mai suna Aliyu Tunde Muhammad Elyaqub ya ja hankalin jama’a bayan ya mayar da kuɗi Naira miliyan 2.2 da aka tura masa bisa kuskure a asusun sa na OPay.
Rahotanni sun bayyana cewa kuɗin, kimanin N2,260,000, sun shiga asusun sa a ranar 3 ga Afrilu, amma cikin gaskiya da amana ya gaggauta mayar da su gaba ɗaya ga wanda ya aiko da su.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 4 ga Afrilu, Aliyu ya nuna hotunan shaidar shigowar kuɗin da kuma rasidin da ke tabbatar da cewa ya dawo da su ba tare da ya rage komai ba.
Bayan mayar da kuɗin, an ce wanda ya aiko masa da su ya yi ƙoƙarin ba shi kyautar N50,000 a matsayin godiya, amma Aliyu ya ƙi karɓa, yana mai jaddada cewa abin da ya yi kawai gaskiya ce da ya kamata kowa ya aikata.
Lamarin ya jawo yabon jama’a a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana shi a matsayin abin koyi na gaskiya da riƙon amana a cikin al’umma.

0 Comments:
Post a Comment