Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin Moscow na kasar Rasha domin gudanar da muhimman tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan batutuwan da suka shafi yaƙi da Ƙasar ta fafata da Israi'la da Amurka da Kuma makomar yankin gulf.
Ziyarar na daga cikin kokarin da kasashen Iran da Rasha ke yi na ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna kan manyan al’amuran siyasa na duniya.
Ana sa ran Araghchi zai gana da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, domin tattauna halin da ake ciki a yankin, musamman bayan tashe-tashen hankula na baya-bayan nan.
Wannan ziyara ta zo ne a karshen rangadin diflomasiyya da ministan ya yi, wanda ya hada da kasashen Pakistan da Oman, inda ya tattauna hanyoyin rage tashin hankali da samar da zaman lafiya.
Jakadan Iran a Rasha ya bayyana cewa kasashen biyu suna da ra’ayi guda kan muhimman batutuwan yanki da na kasa da kasa, lamarin da ke kara karfafa dangantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu.
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karin matsin lamba da rikice-rikicen siyasa a duniya, inda Rasha ke ci gaba da nuna goyon baya ga Iran a fagen kasa da kasa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment