Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci taron makoki a birnin Tehran da sauran birane a fadin ƙasar na cika kwanaki 40 da kashe Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei a harin ta'addancin da Israi'la da Amurka suka kai a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Taron ya samu halartar manyan sojoji da dalibai da yara daga Minab.
An fara taron ne da safiyar yau Alhamis inda taron mutane ya nufi "dandalin Jamhuri" zuwa wurin da aka kashe Ayatollah Khamenei, wanda hukumomin Iran suka bayyana a matsayin harin ta’addanci da Amurka da Isra’ila suka kai.
Mahalarta taron sun yi ta rera waƙoƙi da sauraron jawabai, da kuma sabunta biyayya da mubayi'a ga jagoran.
Makokin kwanaki 40 da ake kiran 'Chehlom' a al’adar Shi’a, tana da muhimmanci sosai a Iran, inda ake bukukuwar nuna girmamawa da jinjina na soja daga taron jama’a a Tehran.
Haka zalika, an gudanar da irin wannan taron a birane da kananan hukumomi a fadin kasar.
Hukumomin sojin Iran sun mayar da martani kan kashe jagoran da harin makami da jiragen sama mara matuki kan Isra’ila da kuma Sansanonin sojin Amurka a yankin gabas ta tsakiya.
Taron ya biyo bayan kwanaki 40 na makoki a fadin kasar da gwamnatin Iran ta ayyana tun bayan rasuwar Khamenei, wanda ya hada da hutu na jama’a da gudanar da ibadoji na addini.

0 Comments:
Post a Comment