Iran ta yi watsi da barazanar Trump kan kulle mashigin Hormuz.

Iran ta yi watsi da barazanar Trump kan kulle mashigin Hormuz.

Shugaban rundunar sojojin ruwa na ƙasar Iran, Shahram Irani, ya yi watsi da barazanar tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, kan yiwuwar kulle mashigin ruwa na Strait of Hormuz, yana mai cewa hakan “abin dariya ne kuma ba zai yiwu ba.

Rahotanni sun nuna cewa Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya kulle mashigin Hormuz bayan da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta gaza.

Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin ruwa a duniya, inda ake jigilar kaso mai yawa na man fetur na duniya ta cikinsa.

A nasa martani, Shahram Irani ya bayyana cewa: Iran ba ta ɗauki wannan barazana da muhimmanci ba, kuma Rundunar ruwan ƙasar na sa ido kan duk wani motsi a yankin.

Saboda haka duk wani yunƙuri na kulle mashigin zai fuskanci martani mai tsauri.

Mashigin Strait of Hormuz Hanya ce mai matuƙar muhimmanci ga safarar mai, yayi da masana ke gargadin cewa duk wani rikici a yankin na iya haifar da tashin farashin mai a duniya

Mashigar ruwan Hormuz Yana da tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin ƙasashe da dama.

Rikicin kalamai tsakanin Amurka da Iran na ci gaba da ƙara zafi, yayin da ɓangarorin biyu ke nuna ƙarfin iko. Duk da haka, ana fargabar cewa duk wani kuskure na iya haifar da babban rikici a duniya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: