Gwamnatin Birtaniya Ta Haramta Shan Taba Ga Wadanda Aka Haifa Bayan shekara 2008.

Gwamnatin Birtaniya Ta Haramta Shan Taba Ga Wadanda Aka Haifa Bayan shekara 2008.

Gwamnatin Birtaniya ta amince da wani sabon kudiri na doka da zai hana duk wanda aka haifa bayan ranar 1 ga Janairu, 2009 sayen taba har abada.

Sabuwar dokar na da nufin samar da al’umma marar shan taba a nan gaba, ta hanyar kara shekarun da ake bukata kafin sayen taba a kowace shekara.

Duk wanda yanzu bai kai shekara 18 ba ba zai taba samun damar sayen taba a dokance ba.

Mahukunta sun ce wannan doka na daga cikin manyan matakan kiwon lafiya da aka dauka domin rage mace-macen da ke da nasaba da shan taba da kuma kare matasa daga kamuwa da jarabar nicotine.

Za a rika kara shekarun da ake bukata kafin sayen taba daga shekara 18 zuwa sama a hankali.

Shan taba da kansa ba laifi ba ne, amma sayar da shi ga sabbin matasa zai zama haramun.
Ana sa ran dokar za ta fara aiki daga shekarar 2027 bayan kammala amincewa da ita.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: