Akalla mutane 56, mafi yawansu ‘yan kasuwa, ake fargabar sun mutu, yayin da wasu 14 suka jikkata kuma suke karɓar magani, bayan wani harin sama da aka kai a kasuwar mako-mako ta Jilli- Jilli da ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio a jihar Borno da Geidam a jihar Yobe, a ranar asabar 11 ga Afrilu.
Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa ana zargin harin sama ne da sojoji suka kai yayin wani farmaki da aka tsara domin neman mayakan Boko Haram.
Wannan kasuwa ta mako-mako na jawo ‘yan kasuwa da masu saye daga yankunan da ke kusa da wajen Gubio da Chiweram da Benisheikh a Borno, da kuma Gurokayeya da Geidam a jihar Yobe.
Majiyoyi sun ce jiragen yaki sun bi sawun wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne, wadanda ake kyautata zaton sun shiga kasuwar domin karɓar haraji daga ‘yan kasuwa da kuma neman kayayyaki. Sai dai rahotanni sun ce harin ya kauce wa manufarsa, inda ya fada kan fararen hula da ke kasuwar.
Wani shaida ya ce ya ga akalla gawarwaki 56 sannan ya taimaka wajen kai wasu raunana asibiti a Geidam.
Ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:46 na rana lokacin da harkokin kasuwa ke gudana, inda aka ji ƙarar fashewar abubuwa daga jiragen yaƙi da dama.

0 Comments:
Post a Comment