Dubun-dubatan mutane ne suka fito zanga-zanga kan ziyarar Shugaban Isra’ila Herzog a ƙasar Australia.


Dubban masu goyon bayan Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Australia domin nuna adawa da ziyarar Shugaban Ƙasar Isra’ila, Isaac Herzog, wanda wasu ke zarginsa da tayar da ƙiyayya da kuma kiran aikata kisan kare dangi kan Falasɗinawa.

A birnin Sydney, ‘yan sanda sun yi amfani da feshin barkono (pepper spray) tare da yin artabu da masu zanga-zangar a yau Litinin, yayin da suka yi tattaki suna nuna adawa da ziyarar Herzog. 
Shugaban Isra’ilan yana Australia ne domin halartar taron tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a harin Bondi Beach na bara.

Rahotanni sun nuna cewa dubban mutane sun taru a wani fili a tsakiyar birnin Sydney a yau Litinin, inda aka shirya ƙarin zanga-zanga a birane da garuruwa daban-daban na ƙasar da yamma.

Hukumomi sun gargadi masu zanga-zanga cewa suna fuskantar kame idan suka shiga tattakin daga Sydney Town Hall zuwa Majalisar Dokokin jihar New South Wales, domin yankin yana cikin wuraren da aka ayyana a matsayin wuraren kariya a lokacin ziyarar Herzog.

Wata kotun Sydney a ranar Litinin ta ƙi amincewa da ƙalubalen shari’a da ƙungiyar Palestine Action Group ta shigar, wadda ta nemi a soke ƙuntatawar da aka sanya kan zanga-zangar da suka shirya.

“Mun yi fatan ba za mu yi amfani da iko ba, domin muna aiki kafada da kafada tare da masu shirya zanga-zangar,” in ji Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sandan New South Wales, Peter McKenna, a wata hira da tashar Nine News.

Herzog ya yi jawabi a Bondi Beach

Shugaba Isaac Herzog ya fara ziyararsa ta kwanaki huɗu a Australia ne a Bondi Beach, inda ya ajiye furanni a wurin tunawa da waɗanda suka mutu a harin watan Disamba da ya kashe mutane 15 yayin bikin Hanukkah. 
Ya kuma gana da waɗanda suka tsira da iyalan waɗanda aka kashe.

“Wannan hari ya shafi dukkan ‘yan Australia ne,” in ji Herzog. “An kai hari kan ƙimomi da dimokuraɗiyyarmu ke darajawa — mutuncin rayuwar ɗan Adam da ‘yancin addini da haƙuri da martaba da girmamawa.”

Ya ƙara da cewa, “Na zo nan ne domin nuna goyon baya da zumunci da kuma ƙauna,” inji Shugaban Israi'lan

Baya ga Sydney, inda aka tanadi jami’an tsaro kusan 3,000, Herzog na shirin ziyartar Melbourne da kuma babban birnin Canberra, kafin komawarsa Isra’ila a ranar Alhamis.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: