Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da wasan Tashe na Ramadan a Kano, bisa dalilan tsaro da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin azumin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa ta hukuma, rundunar ta bayyana cewa tarukan Tashe na dare kan haddasa taruwar jama’a da yawan motsi, lamarin da ka iya bai wa masu aikata laifuka damar yin amfani da taron wajen satar wayoyi, tayar da hargitsi, shan miyagun kwayoyi da sauran laifuka.
‘Yan sanda sun ce an dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da Gwamnatin Jihar Kano, a matsayin wani bangare na tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya da doka a duk fadin jihar a cikin watan mai alfarma.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su sa ido kan ‘ya’yansu, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu ya karya doka ko ya tayar da hankula zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
A karshe, rundunar ta tabbatar da cewa ta kara kaimi wajen daukar matakan tsaro, domin ganin al’umma sun gudanar da ibadar Ramadan cikin kwanciyar hankali da tsaro a Kano.
News Translation in English Language.
Police Suspend Ramadan Tashe Performances in Kano Over Security Risks
The Kano State Police Command has announced the suspension of the traditional Tashe performances held during the Ramadan period in Kano, citing security concerns.
According to a statement issued by the command, the decision was taken to prevent potential threats to public safety, as the night-time cultural performances often attract large crowds and increased movement across neighbourhoods. The police noted that such gatherings could be exploited by criminal elements to engage in phone snatching, thuggery, drug abuse and other unlawful activities.
The command explained that the suspension followed consultations with the Kano State Government as part of broader measures to ensure peace and order throughout the holy month of Ramadan.
The Commissioner of Police also urged parents and guardians to closely monitor their children and wards, warning that anyone found violating the directive or engaging in acts capable of disturbing public peace would be dealt with in accordance with the law. The police assured residents that adequate security arrangements have been put in place to guarantee a peaceful Ramadan season across the state.
Tags
Labarai
