Mutum Huɗu Sun Mutu a Hatsaniya Lokacin Raba Zakkar watan Ramadan a Katsina.

Mutum Huɗu Sun Mutu a Hatsaniya Lokacin Raba Zakkar watan Ramadan a Katsina.

Aƙalla mutum huɗu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hatsaniya  da ta auku a lokacin raba sadakar Ramadan (Zakka) a unguwar Kofar Guga da ke cikin birnin Katsina.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Laraba, 26 ga Fabrairu, 2026, a gidan wani attajiri da ya shirya rabon taimakon Ramadan. Rahotanni sun ce taron jama’a ya yi yawa fiye da kima, lamarin da ya haddasa cunkoso da hatsaniya yayin da mutane ke ƙoƙarin karɓar taimakon.

A sakamakon haka, mutane da dama sun fadi saboda matsalar numfashi, inda huɗu daga cikinsu suka mutu bayan an garzaya da su asibiti. Akalla mutum 18 kuma sun jikkata, wasu daga cikinsu an kwantar da su a Babban Asibitin jihar Katsina, yayin da aka tura wasu masu rauni mai tsanani zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin ƙarin kulawa.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta sun isa wurin cikin gaggawa domin dawo da doka da oda a lokacin da lamarin ya faru. Rundunar ta ƙara da cewa an fara bincike kan musabbabin hatsaniyar, tare da kiran masu shirya rabon taimakon domin ba da bayani.

‘Yan sanda sun kuma shawarci al’umma da ƙungiyoyi masu shirin gudanar da manyan taruka ko rabon sadaka da su sanar da hukumomi tun da wuri, domin samar da tsaro da dabarun kula da taron jama’a, don kauce wa irin wannan mummunan lamari nan gaba.

News Translation in English Language.

Tragedy in Katsina as Four Lose Lives During Ramadan Charity Distribution

A tragic incident unfolded in Kofar Guga area of Katsina, Katsina State, where four people lost their lives following a stampede during the distribution of Ramadan charity (Zakkat).

The incident occurred at about 9:00 p.m. on Wednesday, February 26, 2026, at the residence of a philanthropist who had organised the annual alms distribution. Reports indicate that a large number of beneficiaries turned up for the exercise, resulting in severe overcrowding and confusion.

Eyewitnesses said the situation escalated when people attempted to force their way forward to receive the charity items, triggering panic and a stampede. Several individuals collapsed in the process, leading to fatalities and multiple injuries.

Medical sources confirmed that at least 18 persons were injured and rushed to health facilities. While some victims received treatment at the General Hospital, Katsina, those with critical injuries were referred to the Federal Teaching Hospital, Katsina for specialised care. Sadly, four of the injured later died.

Confirming the incident, the Katsina State Police Command said security operatives were promptly deployed to the scene to restore order. The police disclosed that an investigation has been initiated to establish the circumstances surrounding the stampede.

The command also cautioned philanthropists and organisations involved in charity distribution to engage security agencies ahead of such events, stressing that proper planning and crowd control are essential to prevent loss of lives in future charity exercises.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form