A jiya Lahadi ne wani mutum ya bude wuta a wani shahararren wurin shan giya a Austin jihar Texas na Amurka, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 2 tare da raunata mutum 14.
Rahotanni sun nuna cewa mai harbin ya fara harbin ne daga cikin motarsa a kan mutane da ke wurin shan giya, kafin ya tsaya ya ci gaba da harbin da bindigan. ‘Yan sanda sun kashe mai harbin nan take a wurin.
Hukumar bincike ta FBI da sauran jami’an tsaro suna gudanar da bincike kan wannan harin a matsayin yiwuwar aikin ta’addanci. Sunce an gano alamun addinin Musulunci a kan tufafin mai harbin da kuma wasu abubuwa a motarsa, duk da cewa hukumomi sun ce har yanzu ba a tabbatar da dalilin aikata harin ba.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake samun rikici tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, wanda ke sa wasu jami’an tsaro suna duba yiwuwar alakar harin da yanayin siyasa na kasa da kasa.
Mutane da dama da suka samu rauni sun isa asibitoci, wasu na cikin mawuyacin hali. Hukumar tsaro ta ci gaba da bincike domin gano cikakken dalilin faruwar wannan harin da tarihin mai aikata shi.
News Translation in English Language.
Austin Shooting Under Investigation as Possible Terror-Related Incident.
On March 1, 2026, a gunman opened fire at a popular bar in Austin’s Sixth Street entertainment district, killing two people and injuring 14 others.
Reports indicate the shooter first fired from his vehicle at people outside the bar before stepping out and continuing the attack on foot with a rifle. Police officers responded quickly and shot the suspect dead at the scene.
The FBI and other security agencies are investigating the incident as a potential act of terrorism. Clothing worn by the attacker and items found in his vehicle contained Islamic-related symbols, though authorities stress that the motive has not yet been confirmed.
The attack coincided with heightened tensions following recent U.S.–Israel military action involving Iran, prompting investigators to explore whether there may be an international or ideological link.
Several victims were hospitalized, some in critical condition, while authorities continue probing the suspect’s background and the circumstances of the shooting.
Tags
Labarai
