Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin sama mara matuki da ake zargin Iran ce ta tura ya kai hari kan tashar mai ta Ras Tanura wadda ke karkashin kamfanin Saudi Aramco a yau Litinin.
Wannan tashar na daga cikin manyan wuraren sarrafa mai a Saudi Arabia kuma tana da muhimmiyar rawa wajen fitar da mai zuwa kasashen duniya.
Harin ya haifar da gobara wanda ya sa aka dakatar da wasu ayyuka a tashar domin kare lafiyar ma’aikata da kayan aiki.
Kodayake babu rahoton mutuwar mutane a farko, wannan harin ya nuna matakin barazana ga manyan ababen more rayuwa na makamashi.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, inda Iran ke kai hari da makaman linzami da jiragen sama marasa matuki kan Israel, kadarorin Amurka, da kuma wasu kasashen Gulf.
Masana tattalin arziki sun nuna cewa rufe ko dakatar da ayyuka a tashar Ras Tanura, wadda ke fitar da kaso mai yawa na danyen mai, na iya haifar da tashin farashin mai a kasuwar duniya. Hakanan, irin wannan harin na iya karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Gulf, Amurka da Israel domin magance barazanar da ke tattare da shi.
News Translation in English Language.
Iranian Drone Strikes Saudi Aramco’s Ras Tanura Oil Facility.
Reports confirm that a drone, reportedly launched by Iran, struck the Ras Tanura oil refinery, operated by Saudi Aramco, on Monday. The facility is one of Saudi Arabia’s largest oil processing centers and plays a critical role in global oil exports.
The attack triggered a fire, prompting authorities to halt some operations at the refinery to protect workers and equipment. While there are no initial reports of casualties, the incident underscores the threats facing vital energy infrastructure in the region.
The strike comes amid a widening escalation in the Middle East, with Iran reportedly targeting Israel, U.S. assets, and several Gulf countries using missiles and drones.
Economic analysts warn that the temporary shutdown of Ras Tanura, which handles a substantial share of Saudi crude exports, could impact global oil prices. The incident may also encourage closer cooperation between Gulf states, the U.S., and Israel in countering regional threats.
Tags
Labarai
