Duk da kisan da aka yi wa Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, masana siyasa na cewa tsarin mulkin kasar bai rushe ba, sakamakon yadda aka gina shi a matsayin wani tsari mai bangarori da dama da ke iya ci gaba da aiki ko da babu jagora guda daya.
Wani rahoto da jaridar Arab News ta wallafa ya bayyana cewa tsarin mulkin Iran, wanda ake kira “mosaic regime”, yana da cibiyoyi masu yawa da ke rarraba iko, domin tabbatar da dorewar gwamnati a kowane hali.
Rahoton ya ce kundin tsarin mulkin Iran ya tanadi hanyoyin maye gurbin jagora idan aka samu gibi, inda ake kafa wani kwamitin rikon kwarya na mutum uku da ke kula da harkokin mulki na wucin gadi. Wannan kwamitin ya kunshi shugaban kasa, shugaban bangaren shari’a, da wani babban malamin addini daga Majalisar Kwararru.
Masana sun ce, ko da yake kisan Khamenei abu ne mai girma da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar, tsarin da aka gina tsawon shekaru ya bai wa Iran damar ci gaba da tafiyar da mulki ba tare da tangarda nan take ba.
Rahoton ya kara da cewa har yanzu ba a bayyana sunan wanda zai gaji Khamenei a hukumance ba, amma ana sa ran Majalisar Kwararru za ta taka muhimmiyar rawa wajen zaben sabon jagoran kasar.
A cewar masu sharhi, kalubalen da Iran ke fuskanta a yanzu ba wai kawai neman magaji ba ne, har da yadda za ta shawo kan matsin lamba na waje, rikicin siyasa, da tasirin kisan jagoran a zukatan al’umma da makwabtan yankin Gabas ta Tsakiya.
Jaridar ta kammala da cewa, duk da girgizar da kisan Khamenei ya haifar, tsarin mulkin Iran na da karfin da zai ba shi damar ci gaba da wanzuwa, a kalla a nan gaba kusa.
Tags
Labarai
