Sheikh Alƙali Zariya ya bayar da haƙuri game da dakatarwar da Kungiyar Izala ta yi mashi Daga gudanar da Tafsirin Alƙur’ani a Damaturu.


A ranar Talata ne 03 March, 2026, Ƙungiyar Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) reshen Damaturu a Jihar Yobe ta sanar da dakatar da Sheikh Alƙali Zariya daga ci gaba da gudanar da tafsirin Alƙur’ani a Masallacin Mokas.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan da aka fahimtar da malamin wasu kurakurai da yake aikatawa a yayin karatunsa na tafsiri. 
Sanarwar ta ce bayan tattaunawa da shugabannin ƙungiyar, Sheikh Alƙali Zariya ya amince da kuskurensa, tare da bayar da hakuri ga dukkanin waɗanda abin ya shafa.

JIBWIS ta ƙara da cewa dakatarwar ta zo ne domin tabbatar da bin ƙa’idojin koyarwar addini da kare sahihancin tafsirin Alƙur’ani, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi a Damaturu da ma Jihar Yobe baki ɗaya.

News Translation in English Language.

JIBWIS Suspends Sheikh Alkali Zariya from Qur’anic Tafsir in Damaturu.

On Tuesday, March 3, 2026, the Damaturu branch of Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) in Yobe State announced the suspension of Sheikh Alkali Zariya from continuing Qur’anic tafsir (exegesis) at Masallacin Mokas.

In a statement issued by the organisation, it said the decision was taken after the cleric was cautioned over certain errors identified during his tafsir sessions. The statement added that following discussions with the leadership of the organisation, Sheikh Alkali Zariya acknowledged his mistakes and offered an apology to all those affected.

JIBWIS further explained that the suspension was intended to ensure adherence to established religious teaching standards, protect the authenticity of Qur’anic interpretation, and promote peace and unity among the Muslim community in Damaturu and across Yobe State as a whole.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form