Wasu shugabanni da masu sharhi a Amurka da Isra’ila na ci gaba da bayyana rikicin da ke ƙara kamari tsakaninsu da Iran a matsayin yaƙin addini, ba wai rikicin siyasa ko na tsaro kawai ba.
Wani rahoto da Al Jazeera ta wallafa ya nuna cewa wannan salon bayani na addini na da nufin ƙarfafa goyon bayan jama’a da halatta hare-haren soji da kuma jawo tausayi daga mabiya addinai a cikin gida da waje.
Masana da aka tattauna da su a rahoton sun bayyana cewa sanya rikicin cikin tsarin addini na iya haifar da tunanin “mu da su” a cikin Al'umman duniya, lamarin da ke ƙara tsananta gaba da hana hanyoyin sulhu da warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa amfani da kalmomin addini wajen bayanin yaƙi kan ƙara zafafa ra’ayin jama’a, tare da dasa tunanin cewa ana aiwatar da wani aiki na “umarnin Ubangiji”, wanda hakan kan sa yaƙi ya zama mai wahalar dakilewa.
Masana sun yi gargaɗin cewa irin wannan tsari na bayanin kalmomin Addini na iya ƙara tsawaita rikici a Gabas ta Tsakiya, tare da janyo mummunan tasiri ga zaman lafiya da tsaron duniya baki ɗaya.
News Translation in English Language.
Why the United States and Israel Are Framing the Ongoing Conflict as a Religious War?
Political leaders and commentators in the United States and Israel have increasingly portrayed the escalating conflict with Iran as a religious war, rather than a conflict driven solely by politics, security, or strategic interests.
A report published by Al Jazeera explains that this religious framing is being used to mobilise public support, legitimise military action, and strengthen political narratives at home and abroad.
Analysts quoted in the report argue that presenting the conflict in religious terms creates a stark “us versus them” mentality, which deepens hostility and makes diplomatic solutions more difficult to achieve.
The report further notes that invoking religious language in times of war can harden public opinion, reinforcing beliefs that the conflict is divinely justified or morally absolute. Such narratives, experts warn, often entrench wars rather than pave the way for compromise or peace.
Observers caution that continuing to frame the confrontation in religious terms risks prolonging instability in the Middle East and could have far-reaching consequences for regional and global security.
Tags
Labarai
