Ta tabbata DR Congo ce za ta wakilci Afrika a wasannin tantancewa na cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026, ba Najeriya.

Ta tabbata DR Congo ce za ta wakilci Afrika a wasannin tantancewa na cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026, ba Najeriya.

FIFA ta tabbatar da DR Congo a matsayin wacce zata wakilci Afirka a gasar tantancewa na cin kofin duniya na 2026, lamarin da ya kawo ƙarshen burin Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya na zuwa gasar kai tsaye.

An shirya gasar tantancewar daga ranar 26–31 Maris 2026 a biranen Guadalajara da Monterrey, na ƙasar Mexico, inda ƙungiyoyi shida za su fafata don samun guraben ƙarshe biyu na gasar cin kofin gasar duniya.

Ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta gabatar da ƙorafi, tana ikirarin cewa DR Congo ta yi amfani da ‘yan wasa marasa cancanta a wasan CAF da ya ƙare 1–1 kafin a tafi bugun fanareti a watan Nuwamban 2025. Duk da haka, FIFA ba ta yi wata sanarwa ba kan janye DR Congo ko bayar da damar Najeriya.

A halin yanzu, Najeriya ba ta cikin jerin ƙungiyoyin da suka tabbata za su shiga gasar cin kofin duniya, yayin da DR Congo za ta wakilci Afirka a gasar tantancewar. 
Duk da cewa har yanzu akwai ƙaramin fata na canjin hukunci daga FIFA, rashin jawabi daga hukumar yana sanya samun damar shiga gasar ya zama ƙalubale ga Kungiyar kwallon kafar Super Eagles yayin da lokacin gasar ke Kara gabatowa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form