Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akalla mutane 66,000 ne suka yi gudun hijira sakamakon tashe-tashen hankula da ke gudana a kan iyakokin Afghanistan da Pakistan. Wannan lamari ya shafi lardunan gabas da kudu maso gabashin Afghanistan.
Rahotanni sun nuna cewa tashin hankali da harbin bama-bamai, da kuma karuwar fadace-fadace sun tilasta wa mutane barin gidajensu cikin gaggawa. Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta bayyana cewa rikicin ya jawo matsaloli ga rayuwar fararen hula, tare da lalata abubuwan more rayuwa da hana isar da taimakon jin kai.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan cewa wannan rikici zai iya kara tabarbarewar yanayin rayuwar fararen hula, inda ake bukatar karin taimako da kulawa daga kungiyoyin agaji da hukumomin kasa da kasa.
Masu lura da al’amura na duniya sun nuna damuwa kan yadda rikicin ke kara ta’azzara, inda suka yi kira ga kare hakkokin mutanen da suka rasa muhallansu da kuma tabbatar da cewa ana basu tallafi cikin gaggawa.
News Translation in English Language.
Nearly 66,000 Displaced by Fighting on Afghanistan-Pakistan Border.
The United Nations has reported that approximately 66,000 people have been forced to flee their homes due to escalating clashes along the Afghanistan-Pakistan border, affecting eastern and southeastern Afghan provinces.
Reports indicate that heavy fighting, shelling, and explosions have driven civilians from their homes, creating an urgent humanitarian crisis. The International Organization for Migration (IOM) stated that the conflict is disrupting essential infrastructure and hindering humanitarian aid delivery.
The UN has warned that the violence is worsening the living conditions of civilians and called for increased support from international organizations and aid agencies.
Global observers have expressed deep concern over the intensifying conflict, urging protection for displaced people and immediate humanitarian assistance for those affected by the crisis.
Tags
Labarai
